Avsnitt
-
Rubutun Hausa
-
Shiri ne kan yadda kabilar Gwari ko Gbagi ke daukar kaya a kafada maimakon kai.
-
Saknas det avsnitt?
-
Shirin ya duba al'adar wasa tsakanin abokan wasa na jini wato dan mace da dan namiji da sauran wasanni da ke tsakanin hausawa da sauran kabilu.
-
Shirin Taba Ka Lshe game da kabilun da suka shiga kurmi daga sassan Najeriya da yarda suke samun cin karo da na kabilar Yarabawa.
-
Shirin ya duba yadda Bahaushe da masu mulkin mallaka suka sauya wa yankuna ya yi tasiri a bunkasar al'adun matunen yankunan da abin ya shafa a Kamaru.
-
Bikin taushen fage da dubban al’ummar garin Tsangaya da ke karamar hukumar Albasu a jihar Kano da ke Najeriya
-
Al'ummar Jamhuriyar Nijar na ci gaba da jimamin rasuwar Alhaji Mahaman Kanta fitaccen dan Jarida kuma wakilin Deutsche Welle na farko a Jamhuriyar Nijar.
-
Ko kun san Kabilar Sayawa a jihar Bauchi da ke Najeriya, na da irin nata tsarin yadda take gudanar da bikin aure? Shirin Taba Ka Lashe
-
Shirin ya duba gasar karatun alkurani da aka shirya a jihar Yobe domin zabo gwarzaye da za su wakilci Najeriya a gasar duniya da ake yi, inda aka samu manyan baki da Sarkin Musulmin Najeriya.
-
Shirin ya duba bikin Hausa Kirista da aka saba gudanarwa a duk ranar 26 ga watan disambar kowace shekara sakamakon kirisimeti. Za mu ji yadda bikin ya samo asali a cikin bukukuwan al'adun Hausawa da ma yadda aka gudanar da shi.
-
Shin kun san tarihin Usman Baba Pategi wanda aka fi sani da Samanja mazan fama a shirin harkokin wasan kwaikwayo a arewacin Najeriya?
-
Ko kun san cewa marigayi Shehu Usman dan Fodiyo ya rubuta tarin litattafan ilimi, shirin Taba Ka Lashe na wannan lokaci ya yi nazari a kai.
-
Kabilar Dagomba guda ce daga cikin kabilun da ke da matukar tasiri a arewacin Ghana kuma ta yi biki nadi a birnin Kolon na Jamus.
-
Yadda al'umma a yankin Hausawa suke fadin sunayen yaransu na farko sabanin yadda aka sani a baya.
-
Shirin ya duba muhimmancin tagwaye a lokacin aure a jihar Gaya ta Jamhuriyar Nijar, inda ake gayyatar 'yan biyu da ke a cikin gari da kewaye domin kawo gudurmuwa a wajen bikin 'yan biyu.
-
Shirin ya nufi masarautar Abzinawa ta yankin Zinder da ke Jamhuriyar Nijar don duba tarihi da kuma al'adun masarautar har ma da irin rawar da take takawa wajen sasanta rikice-rikice tsakanin al'umma.
-
Shirin na wannan lokaci, ya halarci bikin nunin fasahar zane-zane da fenti da rubuce-rubucen ayoyi ko surori da alamomi na tsayuwa ko wakafi ko kuma kowasula irinsa na farko da makarantar al-Kur'ani da take koyar da wannan darasi ta shirya a Kano.
- Visa fler