Avsnitt
-
Kasancewar yanzu kayan masrufi sun yi tsada. An samu hauhawan farashi a dukkan abubuwan da zasu samar da ingantacciyar rayuwa. Menene sabubba sannan ina mafita.
-
A doron ƙasa, mallaka Allah an samu wata nahiyar da idan kayi Sallah a fili bainar jama'a, sai ka biya harajin Euro Ɗari Biyu (sama da Naira Dubu Ɗari da Saba'i a yau da 11/12/2023).
Ga kuma tubka da warwara a aiwatar tsare-tsare da suka yi na Ƴancin ɗan Adam da suke ikirarin yi.
Mu samu damar tattaunawa da Mohammed Moayad al-Rachid da ya zauna a wannan ƙasar don jin yadda ya rayu a matsayin sa na Musulmi. -
Yadda muke da Banki don ayijar kudi, akwai hanya da wasu masu himma suke amfani da ita wajen tanada abinci don taimaka wa mabukata a lokaci da a ke matukar buqata.
Mun tattauna da wani kwararre a fannin noma da kiwo wanda ya kwashe shekaru masu yawa yana aikin gona da ta kai hectare 350. Kuma masani ne kwarai wajen harkar bada tallafi da gudanar qungiyoyin agaza wa gajiyayyu da mabuƙata.
Mun samu zama da Mal. Muzzammil Abdullahi (Abu Nadia) don ƙarin haske akan taimaka wa mabuƙata a halin da muka tsinci kan a wannan duniyar. BANKIN ABINCI -
An samu wani da ya ke ganin ya fi Annabi ilimi da iya adalci, don haka ba abin mamaki ba ne ko yaushe kuma a ko ina, a samu wasu da suke ganin ilimin su ya kai matsayin da hatta Malaman su, ba su ganin su da gashi a ido.
-
Malamai da suka wallafa littafai a baya, sun duba yanayin al'umarsu ne da buqatuwar al'umar tasu ga wannan littafai da suka rubuta, shi ya sa suka wallafa su.
Misali idan ka duba irin su Aqida Wasitiyyah, Aqida Hamawiyyah da su Tadmuriyyah, ai duk daga sunayen garuruwa ne aka basu suna, Ibn Taymiyyah ya wallafa su ne musamman ga mutanen wadannan wurare.
-
Shin laifi ne in kwaikwayi wani?
Akwai wasu sinfin mutane da Shari'a ta yadda in kwaikwaya ne?
Mun tattauwa akan wannan mas'ala ganin cewa musamman matasan, suna duba zuwa ga wasu mutana ne suna kwaikwayon irin rayuwar su.
-
Wannan karo, mu taɓo fanni ne da ta shafar ilimi na Addini da irin kutse da katsalandar da za ka ga wasu na yi a cikin ilimi. Ɗanuwa Mal. Abbas Tijjani ya yi magana kan yadda magabata suke bada ƙima da nuna ladabi ga ilimi. Ku sauraa
-
Yadda muke ƙoƙari wajen ciyar da mabuƙata a watan azumi, da haka muke huɓɓasa wajen ganin mun ciyar a watannin da ba Ramadan ba, da abin ya yi kyau. Abin da zai fi wannan shi ne a gina al'umma wadda adadin wanda ake ciyarwa kullum raguwa suke yi.
-
Wannan ne karo na farko da muka tattauna da macce. Ganin cewa wantan Azumi ya kama, mata da yawa suna dukufa wajen aikin neman Aljanna ta hanyar hidima da gida, miji, yara da kuma babban abin, wato Ibada. Shin wai wadannan
matan, ya ya suke yi ne ganin cewa kema Allah Ya azurta ta da aure, yarinya kuma tana kasuwancin ta?
Ku saurari tattaunawar mu da Fatima Zarah Maitambari
-
Yadda watan Ramadan ya gabato, yana da kyau a ce mutum ya gama duk wata shiri da ya ke tunanin ya yi yanzu. A wannan tattaunawar, mu yi magana kan wani muhimmin abu da ya kamata a ce mu sani game da Rayuwar mu da kuma Ramadan
-
Yau mutane da yawa suna fifita ra'ayin su abisa abin da Addini ya karantar, yin haka kuma matsalolin da ya ke haifarwa na da yawa.
-
Musulmi mun zama mutane da sai abu ya faru sannan muke neman daukar mataki. Haka kuma na nuna rashin wayewa ne da kuma ci baya. Kamata ya yi a ce kafin abu ya faru, mun riga mun tanada abubuwa da za su tinkari abin. In alheri, alheri in kuma sharri, rigakafi.
Wannan tattunawar ta kawo fukoki fuda biyu da suka kamata ace muna amfani da su.Allah bamu iko gyarawa, amin.
Ayi sauraro lafiya.
-
Mun tattauna yadda al'amura suke yanzu musamman kasancewar lokaci ne na zabe. Shin wai me ya kamata mu yi a matsayin mu na Musulmi? Ina muka dosa sannan gaba wace irin shiri zamu yi ne?
Saurara ku ji hirar ta mu.
-
This discussion was centered on Muslims and the way they go about their daily lives and the impact this has on how people regard their religion of Islam. The reality is that a lot people form their perception and judgement of Islam on the way they see Muslims behave. So the big question is HOW ARE YOU REPRESENTING ISLAM? Two powerful stories were told in the episode relating to how Islam is represented and alternatives are given where relevant. The highlight of this podcast is for all Muslims to be aware that they are representatives of the Deen in the public realm. Enjoy listening!
-
In this podcast, we explored the major reason why people are lacking when it comes to the issue kindness, also we spoke about some of the benefits that comes with being kind as Islam teaches.
-
Shin wa menene mahangar Addini akan yancin haqqin Dan Adam da ake ta magana? Saurari wannan tattaunawa don samun haske akan wannan maudu'i
-
Idan kana so ka samu rayuwa mai dadi, Maza maza ka saurari wannan don cikin mintoci kadan, mun tattauna yanyar samun irin wannan rayuwar.
-
Sai mu ji ana ce wai jari hujja, to shin hakan kuskure ne ko dai bamu fahinci abin a ne.
-
Shin wasu fannonin ilmuka aka bar musulmai a baya da ya kamata su farka. Akwai bambanci tsakanin ilimin fiqihu da ilimin da na kiwon lafiya da sauran su?
-
Shin akwai rawar da malamai ya kamata su taka a yanayin yadda ake siyasa a yau, ba wannan ba ma, shin ya kamata malamai su shiga siyasa kuwa? Wai menene Zuhudu sannan malamai kaɗai aka sani da zuhudu? Aibi ne idan aka samu malami ya yi Kuɗi? Don samun ansar waɗannan tambayoyi, saurari wannan shiri...
- Visa fler