Avsnitt
-
Matsalar tsaro na daga cikin batutuwan da suka hana kasar nan cikas a ‘yan shekarun nan.
Kuma kamar yadda alumma ke bayyanawa akwai karancin jami’an tsaro da ya kamata ace suna lura, tare da kiyaye rayuka da dukiyoyin alumma a koda yaushe.
Karancin jami’an tsaron ne ya sa wasu daga cikin jihohin da rashin tsaron yafi kamari suka samar da wasu jami’an tsaro dake taimaka wa jami’an tsaron gwamnati wajen dakile haren haren da yan ta’adda ke kaiwa a wasu yankunan kasar nan.
Shirin Daga Laraba na wannan mako zaiyi duba ne kan wannan batu. -
An daɗe ana muhawara, musamman a Arewacin Najeriya, a kan buƙatar yin garambawul ga tsarin makarantun tsangaya.
A baya dai waɗannan makarantu kan samar da mahaddata alqur’ani waɗanda kuma sukan dogara da kai
Sai dai a wannan zamani, yaran da suke karatu a ƙarƙashin tsarin sun zama mabarata.
Gwamnatoci da dama dai sun yi kokarin yin garambawul ga yadda ake gudanar da tsarin, amma ga alama haƙa ta kasa cimma ruwa.
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi Nazari ne kan hanyoyin da za a bi don magance matsalolin da suka dabaibaye harkar. -
Saknas det avsnitt?
-
A zamanin nan, ana alakanta almajirai da bara – hasali ma a lokuta da dama akan yi amfani da kalmar “almajiri” idan ana nufin mabaraci.
Amma a da ba haka lamarin yake ba – almajiri bay a bukatar yin bara ko roko kafin ya sami na sakawa a bakin salati.
Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi nazari ne a kan yadda almajirci ya sauya salo a wannan zamani da ma irin halin da almajirai suka tsinci kan su a ciki. -
Kalmar almajiri ta samo asali ne daga yaren larabci wato almuhajir, dake nufin wanda ya bar garin sa don zuwa wani gari neman ilimi.
Mafi yawan alummar arewa inda akafi sanin Kalmar sun taso ne sun ga ana gudanar da karatun allo ko almajirci, wanda hakan ke nufin almajirci ya samo asali ne tun lokacin da musulunci ya fara shigowa Najeriya daga garin Maidugurin Jihar Borno zuwa kasar Hausa.
Shirin Daga Larab na wannan mako yayi duba ne kan tarihin almajirci da kuma yadda yake a da can baya. -
Taron da Kungiyar Gwamnonin Arewa (NGF) ta yi a Kaduna ya bar baya da kuria’a.
Daya daga cikin shawarwarin da gwamnonin suka yanke ita ce ta kin amincewa da wani Kuduri da Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya kai Majalisar Dokoki ta Kasa.
Shin kishin Arewa ne ya sa gwamnonin suka yi Allah-wadai da Kudurin ko kuma son zuciya?
Wannan ce muhawarar da ta biyo bayan sanarwar bayan taron na NGF, kuma shirin Daga Laraba zai lalubo amsarta. -
Tarbiyya kamar yadda aka san ta a al’adance tana inganta ne idan al’umma gaba daya ta hada hannu wajen ladabtar da yara.
Duk wanda ya kai shekaru talatin zuwa sama ya san cewa a da can iyaye da sauran jama’ar gari suna iya daukar tsumagiya don ladabtar da shi idan ya kauce hanya.
Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi duba ne kan alfanun ko illar hakan wajen ladabtar da yara. -
Afrika na da dadadden tarihin girmama na gaba, musamman dattawan da ke cikin al’umma.
Sai dai a wannan zamani akan samu matashi ya shafa wa idonsa toka ya fito bainar jama’a yana musayar zafafan kalamai da sa’o’in mahaifinsa.
Shin me ya sa ake samun irin wannan?
Don jin amsar wannan tambaya da ma wasu sai ku biyo mu a cikin shirin Daga Laraba na wannan makon. -
Sau da yawa akan samu rashin fahimtar juna a duk lokacin da wata mu’amala ta haɗa mata.
Misali, a asibiti wajen haihuwa mata sun sha kokawa da yadda suke ce ’yan uwansu suna nuna musu rashin tausayi.
Shirin Daga Laraba zai tattauna a kan wannan lamari, ya kuma auna shi a kan mizanin magamar da matan kan yi cewa “Ciwon ’ya mace na ’ya mace ne”. -
Wata muhawara da ta karade shafukan sada zumunta a kwanakin nan ita ce ko ’yan Arewa, musamman Hausawa, suna fita kasashen waje.
Duk da wannan ba wani sabon abu ba ne, batun ya dauki sabon salo ne a shafukan sada zumunta, musamman Facebook da TikTok, inda ’yan kudancin Najeriya suke wallafa fayafayen bidiyo suna tambayar: shin Hausawa suna zuwa kasashen waje?
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne kan wannan batu. -
Yanayin tattalin arziki da ma wasu dalilai kan tilasta wa mutane da dama, ciki har da masu karbar albashi a karshen wata, neman wata hanya ta daban dake kawo Karin kudade.
Shin mene ne yake kawo hakan, kuma mene ne tasirinsa a kan rayuwar masu buga-bugar da ma al’umma?
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi duba ne a kan irin buga-bugar da ’yan Najeriya suke yi don sama wa kansu mafita. -
Sama da mako guda ke nan bayan komawa makarantu domin fara sabon zangon karatu a kusan dukkanin sassan Najeriya.
Sai dai rahotanni sun yi nuni da cewa, ana samun karancin komawar dalibai makaranta a wasu sassan kasar.
Shirin Daga Laraba na wananan makon zai yi duba ne a kan dalilan faruwar hakan. -
Dangantaka ko alaka a tsakanin Najeriya da China tana ƙara yaukaka, musamman a baya-bayan nan.
Ko a kwanan nan, Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu ya jagoranci wata tawaga zuwa kasar ta China domin halartar taron kyautata alakar kasuwanci tsakaninta da kasashen Afirka.
Shirin Daga Laraba na wananan mako zai tattauna a kan ko mecece ribar ’yan Najeriya a irin wannan dangantakar? -
A duk lokacin da dogon hutun zangon karatu na karshe ya kare, iyaye su kan kasance cikin taraddadin yadda zasu fuskanci komawar Yara makaranta, saboda dumbin bukatu da yanayin ke zuwa dasu.
Shin, me ya kamata, iyaye da masu makantu su fi mayar da hankali a kai, musamman la'akari da irin yanayin tsadar kayayyaki da kuncin rayuwa da ake fama dasu a Najeriya?
Shirin Daga Laraba na wananan mako, zai tattauna ne kan wannan batu na komawa makanta bayan hutun dogon zango.
-
Duk da cewa, a wuni daya ne ake bikin ta, amma muhimman al'adun Hausawa da ake tattaunawa game dasu a ranar Hausa Ta Duniya, suna da tasiri a rayuwar al'umma ta yau da Kullum.
Wata dadaddiyar al'ada da aka san al'ummar Hausawa da ita, ita ce al'adar nan ta fito da Abinci daga gidajen makota, inda ake haduwa aci tare musamman ma a Kullum da daddare.
Shirin Daga Laraba na wananan mako, zai tattauna ne kan muhimmancin wannan Al'ada, musamman la'akari da irin halin da ake ciki yanzu a Najeriya.
-
Majalisar dinkin duniya ta ware ranar 21 ga watan Agusta domin tunawa da wadanda ayyukan ta’addanci ya rutsa da su.
A duk lokacin da mutum ya fada hannun ‘yan ta’adda ko rikicin ta’addanci ya rutsa da su, sukan dade cikin damuwa a ransu.
Shirin Daga Laraba na wannan mako zai tattauna kan wannan rana da abin da ya kamata a yiwa irin wadannan mutane.
-
A Najeriya babban bankin kasa CBN ya bayar da wa’adi ga bankunan domin tara adadin wasu kudade a matsayin jarinsu ko kuma su hade guri daya da masu karamin karfi a bankuna.
A halin yanzu wasu har sun fara hadewa da wasu bankunan, duk da yake ba sabon abu ba ne hadewar bankuna waje guda a Najeriya.
To amma me ke faruwa indan bankunan suka hade? shin lamarin na shafar kwastomomi?
Shirin Daga Laraba na wannan mako zai yi bayani kan abin da ke faruwa a duk lokacin da bankuna suka yi maja a waje da juna. -
Gwamnati na fidda shafukan da ‘yan kasa za su iya neman bashi ko tallafi, a lokaci guda kuma masu zamba ta intanet na bullo da shafukan bogi domin yaudarar al’umma.
Yana da kyau mutum ya iya tantance shafin da za a iya yi masa kuste musamman abin da ya shafi kudi.
Shirin Daga Laraba na wannan makon zai yi bayani kan yadda za ku tantance shafukan intanet na tallafin gwamnati na bogi da na gaske. -
Lokaci na tafiya kuma matasa na turjiya kan shirinsu na zanga-zanga, duk da matakan da gwamnati ke ta dauka.
Ana ta kokarin ganin zanga-zangar ta yiwu cikin lumana, domin kauce wa rikidewa zuwa ta tarzoma.
Shirin Daga Laraba zai tattauna kan hanyoyin da suka kamata gwamnati ta bi domin samun mafita kan zanga-zanga. -
A wannan yanayi na damina kusan kullum wuni ake yi ana tafka ruwan sama a wasu sassan Najeriya.
Akwai masu sana’o’in da sai sun fita za a samu taro da sisi amma kuma babu hali.
Shirin Daga Laraba zai tattauna lan dabarun da ya kamata masu sana’o’i su yi amfani da su domin ganin ruwan sama bai dagula musu lissafi ba. -
Tun bayan janye tallafin man fetur, gwamnati ke ta rarraba kayan abinci ga talakawa domin rage musu radadi.
A wannan makon Shugaban Kasa Bola Tinubu ya bayar da umarin raba tirela 20 ga kowace jiha a Najeriya da Birnin Tarayya duk da wasu na wannan salo ba ya tasiri.
Shirin Daga Laraba ya duba yadda tallafin abincin daga gwamnatin zai magance damuwar talakan Najeriya. - Visa fler